Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Masu Coronavirus a Najeriya Ya Doshi 5000


Sabbin alkaluman da hukumar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya ta NCDC ta fitar, sun yi nuni da cewa mutum 146 sun sake kamuwa da cutar cikin yinin jiya Talata.

Har yanzu dai Legas ce ke kan gaba wajen samun yawan masu dauke da cutar, inda yanzu ta sake samun sabin mutum 57.

Baya ga Legas, jihar Kano wacce ta ke fama da yawan mace-mace a 'yan kwanakin nan ita ma ta samu mutum 27 da suka kamu da cutar.

Ya zuwa yanzu adadin masu cutar ya kai 4,787 a duk fadin kasar.

Adadin masu rasuwa sakamakon cutar shi ma yana dada haurawa, inda a cikin yinin jiya kawai aka samu mutum 8 da suka mutu sakamakon cutar.

Hakan ya mayar da adadin wadanda coronavirus ta kashe zuwa 158.

Masu samun waraka su ma sun kara yawa, inda yanzu Najeriya ke da mutum 959 da suka warke daga cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG