Sabbin alkaluman da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta fitar sun nuna cewa karin daruruwan mutane sun kamu da cutar COVID-19.
A cewar hukumar, mutum 575 ne cutar ta harba a yinin jiya Litinin wanda hakan ya mayar da adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar zuwa 29,286.
An samu sabbin alkaluman da aka samu daga jihohi 19 ne, har yanzu jihar Legas ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar wadda coronavirus ke janyowa, inda yanzu ta sake samun mutum 123. Sai birnin tarayya Abuja da ke bin ta da mutum 100.
Sauran jihohin da aka samu karin wadanda suka kamu da cutar sun hada da Delta-58, Edo-52, Ogun-42, Katsina-24, Bayelsa-23, Rivers-22, Borno-19, Plateau-18, Ondo-18 ,Oyo-17, Kwara-15, Osun-13, Enugu-9, Nasarawa-7, Abia-6, Cross River-5, Kaduna-3, Ekiti-1.
Hukumar ta kuma bayyana cewa mutum 11,828 ne suka warke daga cutar yayin da mutum 654 suka mutu.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 28, 2021
Hukumar DSS Ta Tabbatar Da Kama Salihu Tanko Yakasai
-
Fabrairu 28, 2021
Kayan Masarufu Sun Yi Tashin Gwauron Zabi A Kudancin Najeriya
-
Fabrairu 28, 2021
Lokacin Lallashin Masu Daukar Makami Ya Wuce- Buhari
-
Fabrairu 28, 2021
An Saki 'Yan Makarantar Kagara Da Malamansu
-
Fabrairu 27, 2021
'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 6 Tare Da Sace Wasu 15 A Jihar Neja
Facebook Forum