Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Masu Coronavirus Ya Zarta 16,000 a Najeriya


Sabbin alkaluman da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta fitar sun nuna cewa karin daruruwan mutane sun kamu da cutar COVID-19.

A cewar hukumar, mutum 403 ne cutar ta harba wanda hakan ya mayar da adadin mutanen da suka kamu da cutar zuwa 16,083 a kasar.

Jihar Gombe ce ke kan gaba wajen sabbin yawan wadanda suka kamu da cutar, inda yanzu ta sake samun 73. Sai jihar Legas da ke bin ta da mutum 68.

Sauran jihohin da aka samu karin wadanda suka kamu da cutar sun hada da Kano inda aka samu 46, 36 a Edo, 35 a birnin tarayya Abuja, 31 a Nasarawa, 17 a Kaduna, 16 a Oyo, sai 15 a Abia,.

Sauran jihohin sun hada da Delta mai mutum 13, Borno mai 13, 8 a Plateau, 7 a Niger, 7 a Rivers, 6 a Enugu, 6 a Ogun, 3 a Kebbi, 1 a Ondo, 1 a Anambra, 1 a Imo.

Hukumar ta kuma bayyana cewa mutum 5,220 suka warke daga cutar yayin da mutum 420 suka mutu a jihohi 35 tare da birnin tarayya Abuja.

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG