Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Masu Kamuwa Da COVID-19 a Tsakanin Matasa Ya Rubanya - WHO


Shugaban hukumar lafiya ta duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban hukumar lafiya ta duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus

Yayin da mutane da dama ke ganin cewa COVID-19 ba ta fiye kama matasa ba, hukumar lafiya ta Duniya WHO ta bayar da rahoton karuwar masu cutar a tsakanin matasa.

WHO ta ce an samu karuwar wadanda suka kamu da COVID-19 har ninki uku tsakanin matasa cikin watanni 5 da suka gabata, inda ta dora laifin hauhawar akan rashin kiyaye ka’idar ba da tazara.

Ta kuma kara da cewa, kaso 15% na alkaluman masu cutar miliyan 6 sun harbu ne tsakanin watan Fabrairu zuwa tsakiyar watan Yuli, kuma ya kasance tsakanin masu shekaru 15 zuwa 24.

Kafin karshen watan Fabrairu, alkaluman sun kai kaso 4.5%

Yadda wasu matasa ke shakatawa a bakin wani teku da ke Amurka duk da barkewar annobar Coronavirus
Yadda wasu matasa ke shakatawa a bakin wani teku da ke Amurka duk da barkewar annobar Coronavirus

A cewar Darektan hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Gheberyesus, “mun sha fada kuma za mu sake fadi cewa, matasa ba su tsira daga cutar ba, matasa za su iya harbuwa; matasa za su iya mutuwa kana za su iya yada wa wasu cutar.”

Ya zuwa yanzu akalla mutum miliyan 18.5 ke fama da cutar a duk fadin duniya a cewar Jami'ar John Hopkins.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG