Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Murtala Nyako Yace Anya 'Yan Bindigar Dake Addabar Arewa Maso Gabas Ba Su Da Mataimaka


Wuraren da hare-hare ya shafa a harin da 'yan bindiga suka kai a Adamawa, Fabrairu 4, 2014
Wuraren da hare-hare ya shafa a harin da 'yan bindiga suka kai a Adamawa, Fabrairu 4, 2014

Yayin da adadin wadanda suka mutu ke karuwa, gwamnan yace har yanzu ba a fadawa 'yan Najeriya ko daga ina 'yan bindiga ke samun makamai ba

Yayin da adadin wadanda aka kashe a hare-haren 'yan biniga a yankunan kananan hukumomin Madagali da Michika a Jihar Adamawa ya doshi 33 a cewar wasu majiyoyi, gwamnan Jihar Murtala Nyako yace lallai akwai babbar ayar tambaya a kan yadda mahara suke cin karensu babu babbaka.

Gwamna Nyako yace akwai sakaci ko kuma son kai daga bangaren hukuma, idan ba haka ba kuwa babu yadda 'yan bindigar zasu rika yin abinda suka ga dama.

Gwamnan na Adamawa yace abin bakin ciki ne matuka tun da aka fara wannan tashin hankali, ba a fadawa jama'a inda wadannan bindigogi suke fitowa ba.

Gwamna Murtala Nyako ya ce, "saboda haka wannan abin ya zama, alamomi akwai strategic commanders (kwamandojin tsara dabarun yaki) na Boko Haram a cikin Defence System (ma'aikatu da hukumomin tsaro) namu."

Gwamnan na Adamawa tare da wasu gwamnonin su na shirin jagorancin wani gangamin da al'ummar kasa da kungiyoyin sa kai tare da na al'umma zasu yi a fadin kasar na nuna rashin yardarsu da irin abubuwan da suke faruwa.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG