Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shehun Bama Yace Gwamnatin Tarayya Ba Ta Tsinana Komai Wajen Taimaka Musu


Mutane na kallon bangaren fadar Shehun Bama da ya kone bayan harin Boko Haram a garin Bama, Fabrairu 20, 2014.
Mutane na kallon bangaren fadar Shehun Bama da ya kone bayan harin Boko Haram a garin Bama, Fabrairu 20, 2014.

Mai Martaba Alhaji Kyari Ibn Ibrahim el-Kanemi ya bayyana yadda aka kai harin, ya kuma ce al'ummar masarautarsa sun yanke kauna kan gwamnatin Najeriya zata iya kubuto su daga ukubar da suka shiga.

Mai martaba Shehun Bama, Alhaji Kyari Ibn Ibrahim el-Kanemi, yace a yanzu kam al'ummar kasar Bama sun yanke kauna a kan cewa gwamnatin tarayyar Najeriya zata kawo karshen irin ukubar da 'yan bindiga tsagera suka jefa su ciki.

A lokacin da yake bayani kan yadda 'yan bindigar Boko Haram suka kai farmaki kan garin na Bama da asubahin laraba, Mai Martaban yace a yanzu kam gwamnati ba ta kare kowa, ba ta kare komai.

Yace irin abubuwan nan dake faruwa yanzu a arewacin Najeriya, da a ce a kudanci ne ko a wani bangaren dabam, gwamnatin nan ba zata iya dorewa a kan mulki ba.

Yace su kansu sojojin da aka tura su shawo kan wannan lamarin ba su da wadatar kayan aikin da zasu iya shawo kan wannan abu. Yace bai kamata gwamnatin tarayya ta tsaya tana jin labarai da rahotannin karya da ake mika mata kullum da sunan rahotannin leken asiri ba, domin kamar wadanda ke ba ta wadannan labaran ba su son ta takali wannan lamarin ne.

Shehun na Bama ya ce da za a sa kunne a saurari al'ummar yankin kawai ma, za a iya murkushe 'yan Boko Haram cikin kankanin lokaci.

Shehu Kyari Ibn Ibrahim el-Kanemi yace a ranar da abin zai faru, an samu labari daga kauyukan dake kusa cewa an ga jerin motoci da babura sun doshi Bama, kuma har 'yan banga farren hula ma sun kai rahoto. Amma kuma yayi ta neman manyan hafsoshin soja domin bayyana musu abinda ake ciki, amma duk ya kasa samunsu a waya. Bayan minti 30 ne sai wani ya kira shi a kan cewa an fara jin harbe-harbe kuma an sanya wuta a gidajen lowcost na garin.

Shehun na Bama ya zaga da 'yan jarida inda ya nuna musu irin barnar da 'yan Boko haram din suka yi a garin.
XS
SM
MD
LG