Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Wadanda Guguwa Ta Kashe Na Karuwa a Bangladesh


Irin Barnar Da Guguwar Roanu Ta Yi a Bangladesh

Adadin mutanen da suka mutu bayan da Wata guguwa mai karfi da akawa lakabi da “Roanu”, ta ratsa ta gabar tekun kasar Bangladesh a yau Asabar,na cigaba da karuwa.

Ya zuwa yanzu rahotannin sun ce akalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu a guguwar wacce ke tafe da ruwan sama mai karfi.

Hukumomin kasar sun ce an kwashe dubun dubatar mutane daga gidajensu, inda aka ajiye su a wani waje na wucin-gadi mai tantuna sama da dubu biyu.

Rahotannin sun ce akalla mutane biyar ne suka halaka da farko a gundumomin kudancin kasar, bayan da guguwar ta Roanu tare da ruwan sama ta daidaita gidajen da mafi yawansu an gina su ne da laka.

Wani jami’in ‘yan sanda mai suna Shah Alam, ya gayawa kamfanin dillancin labaran Faransa, cewa ruwan saman ya kuma haifar da zaizayar kasa a yankin Sitakundu da ke Chittagong, inda wata mata da danta suka rasa rayukansu, yayin da kasa ta rufe gidansu.

Yanzu haka hukumar tsaron ruwan kasar ta haramtawa duk wani jirgin daukan kaya yawo akan ruwa, yayin da ake sa ran guguwar za ta lafa da yammacin yau.

XS
SM
MD
LG