Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Wadanda Suka Mutu a Mummunan Harin Somaliya Yanzu Ya Kai 270


Irin barnar da harin ya yi
Irin barnar da harin ya yi

Hari mafi muni da aka kai a Mogadishu babban birnin Somaliya ranar Asabar da ta gabata ya kashe mutan 270, kawo yanzu

Adadin wadanda su ka mutu a wani mummunan hari bam da aka kai da motar daukar kaya ranar Asabar, a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, wanda shi ne harin ta'addanci mafi muni a tarihin kasar, ya kai 270.

Ministan Yada Labaran Somaliya, Abdurrrahman O Usman, ya rubuta ta kafar "twitter" cewa a yanzu adadin wadanda su ka mutu ya kai 276, wadanda su ka ji raunuka kuma wajen 300.

A wasu sakonnin da ya tura ta kafar ta 'twitter,' Usman ya gode ma kasashen Kenya da Habasha da kuma Turkiyya, saboda agajin magunguna da su ka tura ma Somaliya.

Masu zanga-zanga da suka fusata sun game tituna su na ta yin tir da kungiyar al-Shabab. Kungiyar mayakan, wadda ta kan yi ikirarin kai hari a birnin Mogadishu, ta yi tsit ya zuwa yanzu. To amma gwamnatin Somaliya da kwararru kan abin da ya shafi ta'addanci sun yi imanin cewa kungiyar ta al-Shabab ce ta aikata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG