Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutane 25 Ne Suka Halaka Sakamakon Wata Fashewa A Mogadishu.


Wani sojan Somalia yake taimakawa wani da ya ji rauni sakamakon fashewar.

Wasu kimanin 50 kuma sun jikkata sakamakon fashewar da ta auku a wata mararrabar hanyoyi da ake kira zobe.

Mutane akalla 25 ne aka halaka, wasu akalla 50 suka jikkata bayan fashewar nakiyoyi da aka nasa cikin watan motar dakon kaya kusa da wata mahadarar hanyoyi a Mogadishu babban birnin Somalia, kamar yadda jami'an kasar da shadun gani da ido suka yi bayani.

Fashewar data auku kusa da mahadar da ake kira Zobe, inda ake yawan zirga-zirga sai tayu harin kunar bakin wake ne kamar yadda wani jami'in 'Yansanda ya gayawa Muriyar Amurka. Shaidun gani da ido suka ce fashewar ta auku lokacin cinda aka sami tsaigo na zirga-zirga.

Wani wakilin Muriyar Amurka a inda fashewar ta auku ya kidaya akalla gawarwaki 25 lokacinda motocin daukar marasa lafiya take daukarsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG