Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin 'Yan Najeriya da Suka Rasu a Saudiya Ya Haura Fiye da Dari Biyu


Wasu cikin gawarwakin alhazan da suka rasu a Saudiya
Wasu cikin gawarwakin alhazan da suka rasu a Saudiya

Alkaluman kwana kwanan nan da hukumar alhazan Najeriya ta fitar ya sun nuna adadin 'yan Najeriya da suka rasu a Saudiya ayayinda suke jifar Shaidan ya haura fiye da dari biyu da kuma wasu 44 da har yanzu ba'a san inda suke ba.

A taron farko da hukumar alhazan Najeriya ta yi da manema labarai kwamishanan yada labarai na hukumar Dr Sale Okenwa ya bayyana irin matsalar da suka fuskanta wurin tantance daliban Najeriya dake karatu a kasar da 'yan Najeriya da suka je aikin hajji..

Su ma jami'an gwamnatin Saudiya basu taimaka da bayyanan da zasu taimaki sauran kasashe ba da hadarin ya rutsa da alhazansu.

Hukumar tace an tabbatar da mutuwar alhazai 274. Ana kuma bincikar wasu 44 da suma ana istifakin sun rasu. Haka kuma alhazai biyu ne kawai ke karban maganai a asibitocin Saudiya.

Yanzu hukumar ta raba wasu katuna wa wadanda 'yanuwansu suka rasu domin a dauki samfarin jinisu saboda gwada 'ya'yan halitta na DNA da zai bada damar gano hatta kabuburan da aka binne 'yanuwansu.

Alhaji Suleiman Usman Hadeija daraktan shiyoyi da jihohi na hukumar alhazan ya kara bayani akan katukan da aka rabawa 'yanuwan mutanen da suka mutu.

Likitan hukumar Dr Kana yace ko uba ko da ko yar wanda ya mutu za'a iya daukan samfarin jininsu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG