Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: Adadin Wadanda Suka Mutu Na Karuwa


wani yankin Maiduguri da aka 'yan kungiyar Boko Haram suka kai hari

Bayan wani hari da 'yan kunar bakin wake suka kai a Yola, babban birnin Jahar Adamawa, bayanai daga hukumomi na cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu na ci gaba da karuwa.

Rahotanni daga birnin Yola a Jahar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa yawan mutanen da suka mutu a harin bam din da aka kai a kusa da kasuwar Jimeta na ci gaba da karuwa.

Wakilin Muryar Amurka ya ruwaito cewa fiye da mutane 31 ne yanzu haka aka tabbatar da mutuwarsu a wannan hari da aka kai.

“Muna da mutane 31 wadanda Allah ya musu cikawa, wadanda suka jikkata muna da mutane 38 a asibiti, kuma wasu suna cikin mawuyacin hali, wasu kuma har an sallame su daga asibitin.” Inji Alhaji Sa’adu Bello, wani jami’in hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA a Yola.

Ya kuma kara da cewa ana bukatar jini domin an samu karancin sa a dakin adana jinin asibitocin.

“Muna rokon mutane su yi kokari su je asibitocin nan guda biyu su ba da na su gudunmawa domin a samu sauki wajen jinyar wadanda suka jikkata.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jahar ta Adamawa DSP Usman Abubakar ya ce cikin wadanda suka rasa rayukansu har da ‘yan kunar bakin waken.

“A dinga kula da wadanda su ke kai kawo, duk mutumin da ba ka yarda da shi ba, ka yi kokarin ka sanar da jami’an tsaro.” Inji DSP Abubakar.

Ga karin bayani a rahoton Ibrahim Abdulaziz:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG