Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: An kai kunar bakin wake a kasuwar Gombi


Kunar bakin wake a Adamawa

Yau da safe wani dan kunar bakin wake ya tayarda bam a kasuwar buhu dake garin Gombi a arewacin jihar Adamawa.

Dan kunar bakin waken ya yi shigar burtu zuwa cikin kasuwar buhu dake Gombi inda ya tayarda bam.

Tashin bam din ya yi sanadiyar hasarar rayuka tare da jikata wasu da dama. Wanda ya tayarda bam din wai yaro ne karami wanda ya yi shigar mata.

Banda shaidu da suka gani da ido, kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar aukuwar lamarin. Kakakin DSP Abubakar ya bukaci jama'a da su dinga kulawa koina.

Ita ma gwamnatin jihar ta bakin kwamishanan yada labarai Ahmed Sajo ta tabbatar da harin amma bata tabbatar da adadin wadanda suka rasa rayukans ba kodayake wani ganao yace ya ga gawarwaki huhutare wadanda suka jikata aka kai asibiti.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG