Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Harin Kunar Bakin Wake Garin Chibok


Akwai rahotanni masu karo da juna kan maharan maza ne ko kuma mata

A Najeriya 'yan kunar bakin wake sun kashe akalla mutane 10 a garin Chibok, garin nan inda 'yan binidgar Boko Haram suka sace 'yan mata 'yan makaranta fiyeda metan kusan shelkaru biyu yanzu.
Shaidu suka ce wani mahari daya ya tada nakiyoyi yau Laraba a wani wurin duba abeban hawa, yayinda wasu biyu kuma suka tarwatsa kansu a kasuwar dake garin na Chibok.
Sai dai akwai rahotanni masu karo da juna kan ko maharan maza ne ko kuma mata.
Nan da nan dai babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai harin, sai dai farmakin yana da alamun aikin Boko Haram ne, wacce take auna taron jama'a kamar tasha ko kuma kasuwa wajen kai hare hare.

XS
SM
MD
LG