Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: Babu Batun Sauya Sheka Ga Wasu Kusoshin Jam’iyyar PDP


PDP

Yanzu haka an fara cece-kuce a jihar Adamawa game da batun sauya sheka da ake cewa wasu kusoshin jam’iyar PDP a jihar sun yi zuwa jam’iyar APC, batun da su ‘yan PDP ke cewa cewa wannan batu ba gaskiya bane.

A wajen wani taron manema labarai a Yola, wasu kusoshin jam’iyar PDP daga yankin Michikan sun karyata rahotannin cewa sun fice ko zasu fice daga jam’iyar tare da ‘dan majalisar wakilai da cewa yan barandar siyasa ne ke yawo da sunayensu.

Yerima Tizhe Waziri da Alhaji Tukur Mohd Modibbo, sai kuma wasu kusoshin da suka tsaya takara a zaben da ta gabata, sun ce bada yauwnsu ba ake tallar cewa sun canza sheka.

Yankin Michikan dai na cikin yankunan da jam’iyar PDP ta yi kaka-gida a jihar Adamawa to sai dai kuma tun bayan zaben kananan hukumomin da aka yi abubuwa suka soma sauyawa. To ko anya PDP zata kai bantenta kuwa a yankin.

Alhaji Sabo Garta, dake zama shugaban jam’iyar PDP a yankin yace su basu tsorata ba.

Wasu mutane na danganta rikicin cikin gida da ya dabaibayi jam’iyar PDP da zama kanwa uwar gamin sauya shekan da wasu ke yi, batun da sakataren jam’iyar PDP a jihar Adamawan Mr Zira Tumba ke cewa ba haka batun yake ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG