Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: Matakin Da Gwamnati Ta Dauka Kan Ilimi Bai Yi Tasiri Ba


Kungiyar Malaman Jihar Adamawa A Ranar Ma'aikata

Kungiyar malamai ta kasa reshen jihar Adamawa ta ce dokar ta baci da gwamnatin jiha ta ayyana watanni shida da suka gabata bata yi tasiri ba.

Shugaban kungiyar malamai ta kasa reshen jihar Adamawa Kwamrad Rodney Nathan, ya ce kungiyar ta dauki matsayar kasancewar suna binta albashin watanni hudu, kudin alawus na hutu shekara biyar, rashin karin girma a bakin aiki da kuma rashin kyautata muhallin da dalibai za su rika karbar karatu game da ingantattun kayan koyarwa.

Ya kara da cewa tun da aka ayyana dokar ta bacin sau daya suka zauna da bangaren zartaswa kuma kawo yanzu ba a ce da su ci kanku ba.

Da yake wa wakilin sashen Hausa bayanin matakan da suka dauka wajen aiwatar da dokar ta bacin, gwamnan jhar Adamawa Sanata Mohammadu Umaru Jibirilla, ya ce gwamnati ta dauki makaranta ‘daya daga kowace shiyya don kyautata muhallinsu da kyautata jin dadin malamai ta hanyar samar masu da ingantattun kayan aiki da kuma biyansu hakkokinsu.

Wani shugaban makarantar firamare a karamar hukumar Gombi da ke jihar Adamawa da ya nemi a sakaya sunan sa, ya nuna takaicinsa da irin halin da malaman ke rayuwa a ciki na rashin biyan albashi da ta tilastawa wasun su musamman magidanta shiga sana’o’in kamar su barema, awon hatsi da wasu kananan aikace aikace don neman abin sawa a bakin salati.

Kungiyar Malaman Jihar Adamawa A Ranar Ma'aikata
Kungiyar Malaman Jihar Adamawa A Ranar Ma'aikata

Wannan yanayi da malamai ke rayuwa a ciki shi ya sa a bikin ranar ma’aikata ta bana ‘ya’yan kunggiyar malaman suka daga kwalaye dauke da sakoni.

Domin karin bayani ga rahotan Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG