Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ADAMAWA: Nakasassun da Suka Sha Kaye a Zabe Na Zargin an Yi Watsi Dasu


Taron NakasassuNn jihar Adamawa

A Najeriya,yanzu haka nakasassu da suka tsaya a zabukan da suka gabata sun soma kokawa da cewa an yi watsi da su,bayan kafa gwamnati. A wasu jam’iyu kyauta a kaba nakasassu takardar shiga takara da zimmar basu kwarin gwiwa na shiga a dama dasu,yayin da akayi alkawarin basu mukamai ga wadanda suka sha kaye .

A jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya, nakasassu sun taka muhimmiyar rawa a zabukan da suka gabata,da har wasun su ma suka tsaya takara,kodayake akasarinsu sun sha kaye batun da ya sa jam’iyar APC da a cikinta suka tsaya takarar da ma gwamnatin jihar daukan alkawarin cewa ba za’a mance da su a harkokin gwamnati ba.

To sai dai kuma da alamun,alkawurran da aka dauka an soma mancewa dasu lamarin da ya kai har wasu nakasassun da suka tsaya takara kokawa.

Mallam Adamu Aliyu Ngurore wani makoho,na cikin nakasassun da suka tsaya takara a zaben kananan hukumomin da ya gabata,yace su fa basu san makomarsu ba yanzu.

A kwanakin baya ne nema dai gwamnan jihar Adamawa Sen. Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla ya nada wani gurgu ,Abubakar Hosere a matsayin hadiminsa ta fuskar harkokin nakasassu.

To ko anya gwamnati ta san da halin da wadan nan nakasassun da suka tsaya takara ke ciki kuwa? Wannan itace tambayar da na yiwa hadimin gwamnan Abubakar Hosere,wanda yace gwamnati na kokari na ganin nakasassun an dama dasu.

To sai dai a nata martanin jam’iyar APC, wadda a inuwar ta nakasassun suka tsaya takara ta nuna bacin ranta game da shakulatin bangaron da masu rike da madafun mulki ke nunawa kasassun na rashin jawo cikin gwamnati.

Ahmad Lawal sakataren tsare tsare na jam’iyar APC a Adamawa,yace bai kamata a barsu kawai a matsayin masu bada shawara ba.

Ko ma da menene dai,masana na ganin lokaci yayi da su ma nakasassun zasu fito domin a dama dasu a ga irin rawar da zasu taka.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG