Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: Shugabannin Manyan Makarantun da Jami'an Tsaro Sun Yi Taro Akan Tsaro


Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo
Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo

Harin ta'addanci da ake kaiwa jami'o'i kamar na jami'ar Maiduguri ya sa gwamnatin Adamawa ta shirya taron shugabannin manyan makarantu da jami'an tsaro akan yadda zasu fuskanci wannan sabon salon 'yan ta'adda

Kamar yadda alkalumman hukumomin agaji a Najeriya ke nunawa,rayuka da dama ne suka salwanta kama daga na dalibai da ma’aikata biyo bayan sauya salon da yan ta’adda ke yi yanzu na kai kunar bakin wake musamman a jami’ar Maiduguri.

Kuma don daukar matakin kandagarki nema yasa hukumomin tsaro a jihar Adamawa daya daga cikin jihohin da balahirar Boko Haram ta fi shafa a arewa maso gabashin kasar,kiran taron gaggawa da shugabanin jami’o’i da sauran manyan makarantun gaba da sakandare don ankarar dasu kan kalubalen dake tafe.

Bayan kammala taron sirrin,kwamishinan yada labaran jihar Adamawa Ahmad Sajo yace dole a dauki matakin kare kai daga duk wani irin kalubale

Tun bayan tashin bama-bamai a jami’ar Maiduguri hankalin dalibai da kuma malaman jami’o’i, ya soma tashi kamar yadda wasu dake jami’ar kimiyya da fasaha ta Modibbo Adama (MAUTECH),dake Yola suka bayyana.

Shima da yake tsokaci wani tsohon jami’in tsaro da yanzu ke aiki da wata jami’a aarewa maso gabashin kasar da bai so a bayyana sunansa ,ya bayyana matakan da ya kamata a dauka.

Kawo yanzu rayuka da dama ne suka salwanta sanadiyar rikicin Boko Haram da aka shafe kusan shekaru bakwai ana fama dashi,koda yake tuni hankula suka fara kwantawa inda harkoki suka soma komawa kamar da.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG