Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa Ta Ayyana Kwana 3 Domin Zaman Makokin Bachama


Marigayi Hama Bachama

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya ayyana kwana 3 domin zaman makokin Hama Bachama, Honest Stepen, basaraken masarautar Bachama da ke jihar.

Gwamnan ya bayar da wannan umurnin ne a cikin wata sanarwar da sakatarensa kan yada labarai Humwashi Wonosikou ya fitar a Yola.

A cewar sanarwar "za a sassauta dukannin tutoci a jihar daga ranar 29 na wannan watan zuwa 1 ga watan Yuli."

Garin Bachama a jihar Adamawa
Garin Bachama a jihar Adamawa

Hama Bachama mai shekaru 66, ya rasu ne a safiyar Lahadi a garin Numan bayan yayi fama da wani rashin lafiya.

Ya hau karagar mulki ne tun a shekarar 2012, kuma shi ne sarkin Bachama na 28.

An yi jana'izar marigayi Bachama a daren 28 ga watan Yuni a garin Lamurde da ke masarautar Bachama.

Facebook Forum

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG