Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa Ta Dauki Matakin Rage Cunkoso A Gidan Kaso


'Yan kaso masu zaman jiran shari'a.

Yanzu haka daga cikin 'yan kaso dubu 55 dubu 11 kawai aka yankewa hukunci sauran su na zaman jiran tsammani.

A wani yunkurin neman magance cunkuso a gidajen yari hukumomin shari’a a jihar Adamawa sun kaddamar da wata dokar da ta tanadi yanke hukunci akan lokaci. Kamar yadda bayanai ke nunawa matsalar jinkirin yanke hukunci na kan gaba wajen jawo cunkoso a gidajen yarin kasar.

A wajen kaddamar da dokar mukaddashin babban jojin jahar Adamawa Justice Nathan Musa ya yi kira ga lauyoyi da masu shigar da kara, su mike, su kara kaimi, su zage dantse, kamar yadda za ku ji a cikin ci gaban bayanin mukaddashin babban jojin na jahar Adamawa Justice Nathan Musa a cikin rahoton da Ibrahim Abdulaziz ya aiko daga birnin Yola:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:41 0:00
Shiga Kai Tsaye

Wani gidan kaso a cunkuse da masu zaman jiran shari'a.
Wani gidan kaso a cunkuse da masu zaman jiran shari'a.
XS
SM
MD
LG