Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ADAMAWA: 'Yan Sanda Sun Kashe 'Yan Bindiga 6


Makudan kudi da aka kwace daga hanun 'yan bindiga
Makudan kudi da aka kwace daga hanun 'yan bindiga

Rundunar 'yan sandar jihar Adamawa ta ce jami'anta sun kashe mutane shidda masu garkuwan da mutane a jihar adamawa.

Rundunar ta kuma gabatar da wasu masu garkuwan sama da goma, ta kwace kudi Naira miliyan hudu da sab'ain da uku da bindiga nan da a ke kira AK 147, da ma adduna da wukake daga hannunsu a cewar kakakin rundunar 'yan sandar jihar, SP Sulaimani Yaya Guroje.

Bindigogin AK-47
Bindigogin AK-47

Wani daga cikin masu garkuwa da mutanen da 'yan sandar suka kama mai suna Abdullhi Abubakar ya shaidawa Muryar Amurka cewa, sun yi garkuwa da wani yaro sun karbi miliyan hudu da dubu dari biyar amma an bashi dubu dari tara ne kawai a ciki.

Wasu yan bindiga da aka kama
Wasu yan bindiga da aka kama

A hirar shi da Muryar Amurka, Hassan Iro, wani mai garkuwan da mutane a jihar da 'yan sadan su ka kama da bindiga AK-147 a gidansa, ce sama da shekaru biyu kenan yana wannan aikin kuma sun dade suna daukan mutane suna karbar kudin fansa.

Saurari rahoton Salisu Lado a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

XS
SM
MD
LG