Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa Zata Ci Gaba Da Tallafawa Maharba Da Suke Fafatawa Da Boko Haram.


Muslim Kashmir salat Jumat di tepi Sungai Jhelum sambil menjaga jarak aman di tengah pandemi COVID-19 di kota Srinagar, wilayah Kashmir yang dikuasai India.
Muslim Kashmir salat Jumat di tepi Sungai Jhelum sambil menjaga jarak aman di tengah pandemi COVID-19 di kota Srinagar, wilayah Kashmir yang dikuasai India.

Kwamishinan yada labarai na jahar Ahmed Sajoh ne ya bayyana haka, lokacinda yake magana biyio bayan kisan Kwamanda Bukar Jimeta.

Gwamnatin jihar Adamawa daya daga cikin jihohin da yan sakai na maharba ke taimakawa sojoji a yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya,ta sha alwashin cigaba da taimakawa domin kwaliya ta biya kudin sabulu.

Wannan dai ya biyo bayan kisan da mayakan Boko Haram suka yiwa wasu maharba ne ciki har da wani babban kwamandan maharba Bukar Jimeta.

Da take mika jajenta game da wannan rashi na maharban gwamnatin jihar Adamawa daya daga cikin jihohin da yan sakai na maharba ke taimakawa sojoji a yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram a arewa maso gabas,ta sha alwashin cigaba da taimakawa domin kwaliya ta biya kudin sabulu.

Ahmad Sajo dake zama kwamishinan yada labarai da tsare tsare najihar Adamawa,ya ce gwamnati zata cigaba da tallafawa.

Shi dai marigayi kwamanda Bukar Jimeta,da yan Boko Haram suka kashe a fagen daga,kullum cewa yake ba gudu ba ja da baya.

Aisha Gombi dake zama kwamandan mata a kungiyar maharban ta nuna alhininta ne game da rashin da suka yi.

To sai dai kuma duk da wannan rashi da suka yi shugaban kungiyar maharba a jihohin arewa maso gabas Alh. Muhammad Usman Tola kira yake yi ga maharban da kada a ja baya.

Kawo yanzu rayuka da dama ne dai suka salwanta sanadiyar wannan rikici na Boko Haram da aka shafe fiye da shekaru bakwai na fafatawa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG