Accessibility links

Tunda gwamnatin yanzu canji take bukatan kawowa gwamnan yace ya zama wajibi su rage albashinsu domin su tallafawa talakawa.

Gwamna Alhaji Muhammad Umaru Jubrilla Bindo ya roki mukarrabansa da 'yan majalisa su sadaukar da rabin albashinsu ga talakawan jihar.

Yace rage albashin zuwa kashi hamsin zai fara da shi har zuwa kwamishanoninsa domin talakawa su san canji ya zo garesu. Za'a yi anfani da rabin albashinsu ne domin taimakawa wurin aikin rayar da al'umma.

Matakin da gwamnan yace zai dauka ya sa al'ummar jihar sun fara tofa albarkacin bakinsu. Abubakar Babajo tsohon kansila a karamar hukumar Yola ta arewa yace gwamnan ya bada gurbi mai kyau ga sauran masu rike da mukaman siyasa musamman zababbu. Ya kara da cewa kudurin da gwamnan ya dauka babban kalubale ne ga talakawa na sauke hakinsu a matsayinsu na 'yan kasa wajen biyan haraji..

Babajo bai ce gwamnati ta karawa talakawa haraji ba amma su duba yadda zasu tabbatar da biyan harajinsu komi kankancinsa domin su taimaka. Taro sisin nan da ake bayarwa idan sun taru sun zama kudi. Kada a rena. Yace a kara karfi da karfe a taimakawa gwamnatin.

Wani tsohon dan majalisa ya kira talakawa kada su yi wasa. Su ma su sadakar da kai domin a samu cigaba.

Ga rahoton Sanusi Adamu.

XS
SM
MD
LG