Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adeleke Ademola Na Jam'iyyar PDP Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Osun


An ayyana Adeleke Adelemola a matsayin wanda ya lashe zaben jihar Osun
An ayyana Adeleke Adelemola a matsayin wanda ya lashe zaben jihar Osun

An ayyana sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun da aka yi ranar Asabar 16 ga watan Yuli.

WASHINGTON, DC - Adeleke ya samu kuru’u 403,371, inda ya kayar da gwamna mai ci Adegboyega Isiaka Oyetola na jam’iyyar APC wanda ya samu kuru’u 375,027, yayin da Lasun Yusuf na jam’iyyar Labour (LP) ya samu kuru’u 2,729.

“A madadin shugaban hukumar zaben INEC mai zaman kanta, ina ayyana Ademola Adeleke Jackson Nurudeen a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun,” a cewar babban jami’in bayyana sakamakon zabe Farfesa Oluwatoyin Ogundipe na jami’ar Lagos.

Davido (tsakiya) Ademola Adeleke (sanye da shudiyar hula) (Facebook/PDP)
Davido (tsakiya) Ademola Adeleke (sanye da shudiyar hula) (Facebook/PDP)

‘Yan jihar Osun magoya bayan Adeleke sun bayyana farin cikinsu, wasunsu na cewa da ma ba wannan ne karon farko da Adeleke ya ci zabe ba in ba don an yi masa murdiya ba, sun kuma yaba wa hukumar zaben jihar kan kokarin da ta yi a zaben.

Magoya bayan sun kuma yi masa fatan alheri tare da yin kira a gare sa da ya yi aiki yadda ya kamata.

Saurari rahoton Hassan Umar Tambuwal:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG