Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Kokarin Magance Koken Da 'Ya'yan Jam’iyyar PDP Ke Yi - Atiku 


Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowo, hagu da Atiku Abubakar, dama (Hoto: Facebook/Ifeanyi Okowo)
Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowo, hagu da Atiku Abubakar, dama (Hoto: Facebook/Ifeanyi Okowo)

“Muna daukan matakan magance korafe-korafe dukkan mambobin jam’iyya. Hadin kanmu shi ne muhimmin abu a gare ni.

Babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a Najeriya na kokarin lalubon bakin zaren matsalolin da suka kunno kai a jam’iyyar a kwanan nan.

Tun bayan da jam’iyyar ta ayyana gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa, wasu shugabannin jam’iyyar da dama suke ta korafi.

Hakan ya kai ga wasu suke kira da a tsige shugaban jam’iyyar Dr. Iyorchia Ayu.

A ranar 16 ga watan Yuni, dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar, Atiku Abubakar, ya dauki Okowa a matsayin abokin takararsa a zaben 2023.

Sakon Atiku Abubakar

Sai dai cikin wani sako da ya wallafa a ranar Alhamis, Atiku ya tabbatar da cewa jam’iyyar tana kokarin dinke wannan baraka da ta kunno kai, yana mai cewa, za a sasanta komai.

“Muna daukan matakan magance korafe-korafe dukkan mambobin jam’iyya. Hadin kanmu shi ne muhimmin abu a gare ni.

“Burinmu na ganin mun hada kan Najeriya zai fara ne daga jam’iyyarmu zuwa cikin al’umomi da kasa baki daya.” Atiku ya rubuta a shafinsa na Facebook da Twitter.

Rade-radin An Dakatar Da Shugaban Jam’iyya Dr. Ayu

Wani abu da ya kara nuna cewa jam’iyyar na fama da rikicin cikin gida shi ne sanarwar da jam’iyyar ta fitar a ranar Laraba inda ta kore rade-radin da ake yi cewa an dakaar da Dr. Ayu.

“Wannan rahoto babu kamshin gaskiya a ciki, labari ne kawai wasu suka kirkira da niyyar haifar da rudani a cikin jam’iyyarmu.” Sanarwar dauke da sa hannun Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Debo Ologunagba ta ce.

Sanarwar ta kara da cewa, Dr. Ayu ya tafi “wani takaitaccen hutu ne zuwa kasar waje, kuma ya mika ragamar tafiyar da jam’iyyar a hannun mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar arewa, Ambasada Umar Iliya Damagum."

Lokacin da aka zabi Ifeanyi Okowa, hagu, a matsayin abokin takarar Atiku, dama (Hoto: Facebook/PDP)
Lokacin da aka zabi Ifeanyi Okowa, hagu, a matsayin abokin takarar Atiku, dama (Hoto: Facebook/PDP)

Bugu da kari, yayin da ake tunkarar zaben Gwamna a jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya, kwamitin gudanarwar jam’iyyar ta PDP ya gudanar da taro a ranar Laraba kan tsare-tsaren yadda za a tunkari zaben.

Sai dai Gwamnoni biyu ne kacal cikin 13 da jam’iyyar take da su a kasar suka halarci taron, wani da wasu ke nuni da cewa fushi suka yi.

A ranar 16 ga watan Yuli za a yi zaben gwamna a jihar ta Osun.

A 'yan makonnin da suka gabata APC ta lashe zaben jihar Ekiti, inda jam'iyyar PDP ta zo ta uku bayan SDP.

Adawa Da Zabin Ifeanyi Okowa Daga Kudu

Kwanaki biyu bayan da aka sanar da Okowa a matsayin abokin takarar Atiku, gamayyar kungiyoyin kare muradun kudanci da yankin tsakiyar Najeriya da ake kira SMBLF a takaice, ta yi Allah wadai da zabin sa.

A cewar kungiyoyin, amincewa da Okowa ya yi da zabinsa, ya saba matsayar da aka cin ma a ranar 11 ga watan Mayun shekarar 2021, inda gwamnonin jihohin kudancin Najeriya suka yanke shawarar cewa mulki ya koma yankinsu.

“Abin mamakin shi ne, Gwamna Okowa ne ya jagoranci zaman da aka cin ma wannan matsaya mai cike da tarihi. Sannan gwamnonin sun hadu a ranar 5 ga watan Yulin bara a Legas, inda suka kara jaddada wannan matsaya.” Sanarwar gamayyar gwamnonin kudancin Najeriya ta ce.

Wasu gwamnonin jihohin kudancin Najeriya (Hoto: Facebook/Babajide San Olu)
Wasu gwamnonin jihohin kudancin Najeriya (Hoto: Facebook/Babajide San Olu)

Gwamnonin kudancin na Najeriya sun ayyana amincewar da Okowa a matsayin cin amanar yankin.

Ko da yake, kungiyoyin dama daga yankin Niger Delta sun ayyana zabin Okowa a matsayin abu mafi a'ala da zai taimaki yankin kudancin kasar baki daya.

A kuma ranar Laraba ne tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya raba gari da zabin tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku, wanda jam’iyyar ta tsayar a matsayin dan takarar shugaban kasa a 2023.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Fayose wanda shi ma ya nemi tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta PDP, ya ce kudu ce ya kamata ta fitar da dan takara ba arewa ba.

‘Shugaba mai ci a yanzu wanda ya ke shirin kammala wa’adi na biyu daga arewa yake, abin da ke nuna cewa, ya kamata shugabancin kasar ya koma kudanci a 2023.” Fayose ya ce.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar

Bayanai sun yi nuni da cewa shugabannin jam'iyyar ciki har da Atiku, sun tashi tsaye wajen ganin sun dinke wannan baraka da ke ci gaba da fadada.

“Jam’iyyar PDP za ta ci gaba da kasancewa dunkulalliya...…muna daukan matakan magance korafe-korafen dukkan mambobin jam’iyyar.”

Wannan rikicin cikin gida na babbar jam’iyyar ta adawa na faruwa ne a yayin da ita kanta jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC,) take fuskantar nata matsalolin.

A ranar Talatar da ta gabata, Shugaba Buhari ya karbi bakunci sanatoci 22 da ke barazanar komawa jam’iyyar PDP saboda rashin gamsuwa da suka nun kan yadda aka yi zabukan fitar da gwani a jihohinsu.

Ire-iren wadannan rikice-rikicen cikin gida a siyasar Najeriya, abu ne da ke bayyana a duk lokacin da aka zo yin babban zabe a kasar, lamarin da kan kai ga wasu su yi wa jam'iyyunsu zagon kasa ko su yi wa wasu jam'iyyu sojan gona.

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG