Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Kai Wasan Karshe; Ta Yi Rawar Gani A Gasar Afrika Ta U20-M'Boge


'Yan wasan Ghana U20

Kocin zakarun ‘yan wasan Gambia kasa da shekaru 20, Mattar M’Boge ya yaba wa ‘yan wasan Ghana biyo bayan wasan kusa da na karshe da kungiyar ‘yan wasan Ghana, Black Satellites din ta yi da yammacin ranar Litinin.

Zakarun ‘yan wasan kasa da shekaru 20 na Ghana sun yiwa Young Scorpios ci daya mai ban haushi a filin Stade Olympique a birnin Noakochott.

A daidai minti 34 da wasan ne Percious Boah na Ghana ya dauko bugun tazara ya zura kwallo a raga, kwallon da ta kai Ghana da ta lashe kofin Afrika sau uku kana ta yi wasannin karshe sau shida nasarar kai ga wasan karshe.

Kocin Gambia ya tabbatar cewa “ganin cewa za mu hadu da babbar kungiyar wasa ta Ghana, wacce ita ma ta yi damara, mun kimtsa sosai a wannan fafatawa.”

“Amma haka wasan kwallo ya gada, muna alfaharin cewa mun hana Ghana sakewa ta yi wasan da take so da Gambia.”

“A karshe dai mun koyi darasi sosai, ya ce muna yi wa Ghana fatan alheri a wasanta na gaba a wannan gasar.”

Ghana zata fafata da Uganda a wasan karshe na gasar zakarun Afrika kasa da shekaru 20, yayin da Gambia za ta raba rana da Tunisia a wasan neman gurbi na uku na gasar.

AFCON 2021, Super Eagles

Yan wasan Najeriya na atisaye gabanin karawar da za su yi da Guinea-Bissau a rukunkin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021: Troost-Ekong

Kowa ya san cewa mun iya taka leda’ In ji Troost-Ekong, yayin da Najeriya ta kai zagayen knockouts
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG