Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AFGHANISTAN: Mayakan Sama Sun Kashe Sama Da Mutane 30 A Taron Addini Tare Da Jikata Wasu


Jiragen mayakan yakin Afghanistan
Jiragen mayakan yakin Afghanistan

Sama da mutane 30 ne mayakan saman Afghanistan suka kashe tare da jikata wasu 51 a wani farmaki da suka kai kan wani taron addini

Rundunar mayakan sama ta Afghanistan ta kai farmaki a wani taron addini ta kashe akalla yara 30 kana kuma raunata wasu 51 a watan da ya gabata, a cewar sakamakon wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da aka fitar jiya Litinin.


Gwamnatin Afghanistan tace tana kokarin auna shugabanin Taliban ne, ciki har da mambobin Quetta Shura, shugabanin kungiyar dake zama a Pakistan.


MDD bata tabbatar da ko akwai wasu manyan shugaban Taliban a wurin taron ba. Sai dai shedun gani da ido sun fadawa masu bincike na MDD cewa wasu yan Taliban sun halarci taron, wasun ma sun yi aiko samar da tsaro a wurin taron.

A halin da ake ciki kuma, haren haren da mayakan sakai suka kai kan jami'an tsaron kasar a karshen makon jiya ya halaka jami'ai 252, wasu 400 suka ji rauni. Kususshohin gwamnatin kasar ne suka shaidawa majalisa haka, don nuna tabarbarewar tsaro a kasar.


Wannan ne karon farko a cikin watanni da dama da jami’ai suka bada sanarwar kisa mai dimbin yawa da aka yiwa jami'an tsaron kasar Afghanistan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG