Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taliban Ta Mamaye Anar Dara A Afghanistan


Anar Dara, Afghanistan
Anar Dara, Afghanistan

Kungiyar taliban ta mamaye wata gunduma a yammacin Afghanistan, kusa da iyakar kasar da Iran bayan da suka yiwa dakarun gwamnatin kasar mummunar illa.

A cewar wani mai magan da yawun gwamnatin yanki yayi, yace 'Yan bindiga sun kai hari a Anar Dara dake lardin Farah a safiyar yau litinin har suka mamaye wani bangare na babban birnin Lardin.

Nasir Mehri, ya shaidawa muryar Amurka cewa har yanzu ana ci gaba da gwabza kazamin yaki a yankin, inda sojojin gwamnati ke ci gaba da rike sansanonin su da hukumomin ar leken asiri.
An aika da sababbin sojoji da mayakan sama zuwa yankin mai tsaunuka, amman 'yan talliban sun bibbine nakiyoyi kan hanyoyi zuwa Anar Dara, abinda ya janyo cikas ga dakarun kasa, wadand asuke kokarin kaiwa ga Ana Dar.

Mai magana da yawun sojojin cikingida a kabuk ya tabbatar da mutuwqar sojojin Afghanistan a kalla guda 8 inda yace harin maida martani da suka kai ta sama ya kashe akalla 'yan bindiga 60.

Kungiyar taliban sunyi ikirarin cewa sunada cikakken iko kan yankin da hedkwatar 'yansanda da ma zagayen shi.

Mai magana da yawun 'yan bindiga Qari Yousuf Ahmadi ya tabbatar da cewa an kashe sojojin SAfghanistan 15 kuma sun kwace motocin sojojin da kayan yaki, taliban kuma ta saki hoto wanda ke nuna sojojin ta na zirga zirga a titunan garin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG