Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afghanistan: Ministan Tsaro da Hafsan Sojoji Sun Yi Murabus


Hafsan sojoji Qadam Shah Shahim da Ministan Tsaro Abdullahi Habibi da suka yi murabus
Hafsan sojoji Qadam Shah Shahim da Ministan Tsaro Abdullahi Habibi da suka yi murabus

Mummuman harin da kungiyar Taliban ta kai wani barikin sojin kasar Afghanistan ya sa ministan tsaro da hafsan sojojin kasar yin murabus daga mukamansu

Ministan tsaro da kuma Shugaban Sojojin Afghanistan sun ajiye mukamansu biyo bayan mummunan harin da aka kai akan wata babbar barikin sojojin wanda yayi sanadiyyar mutuwar akalla sojoji 140 da kuma jikkata wasu da dama.

Kungiyar Taliban itace ta dauki alhakin wannan mummunan hari akan Bataliyar Soji ta 209 mai suna Shaheen Corps dake Arewacin birnin Mazar-e-Sharif.

A wata gajeriyar sanarwa ofishin Ghani yace “Ministan Tsaro Abdullah Habibi da kuma Shugaban Sojoji Staff Qadam Shahim sun ajiye mukamansu nan take” kuma shugaban kasa ya karbi saukar tasu.

Daga baya Habibi tare da Shahim sun fadawa taron manema labarai cewa sun sauka ne da kansu ba wai tilasta musu aka yi ba.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG