Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Gwamnan Jeka-Nayi-Ka Na Lardin Baghlan Dake Afghanistan


Reshen kungiyar Taliban dake Afgahnistan, ya tabbatar da cewa yayin wani samamen hadin gwiwa da dakarun tsaron NATO, da sojojin kasar suka kai, an kashe wani shugabansu dake Lardin Baghlan a daren jiya Talata.

A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, Kakakin Taliban, Zabihullah Mujahid ya ce Mawlawi Lal Mohammed ya mutu tare da wasu mayaka hudu yayin wani harin sama da aka kai a yankin Dand-e-Ghori.
Haka kuma Kakakin dakarun Afghanistan na musamman, Ahmad Jawed Saleem, ya tabbatar an kashe ‘yan Taliban 15.
Shi dai Mohammed ba shi bane shugaba ko kuma gwamnan jeka-na-yi-ka na farko da dakarun kasar suka kashe a wannan shekarar.
Dakarun na NATO, da dakarun Afgahnistan sun kashe Kundoz Mullah Abdul Salam a watan Fabrairun wannan shekarar.
Wannan farmakin na zuwa ne kwanaki kadan bayan wata ziyara da mai baiwa shugaban Amurka shawara kan harkar tsaro, H.R McMaster ya kai yankin, inda ya yi alkawarin cewa Amurka za ta taimaka wajen karfafa dakarun kasar ta Afgahnistan, musamman ma bangaren sojojin sama.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG