Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AFGHANISTAN: Shugaban Kungiyar Taliban Ya Mutu


Mullah Omar

Kungiyar Taliban a Afghanistan, da kuma wasu majiyoyi kusa da kungiyar 'yan tawayen gameda taron sulhu tsakaninta da gwamnatin Afghanistan, da ake shirin yi a Pakistan cikin makon nan, suna karyata rahotannin da suke cewa shugaban kungiyar Mullah Omar, wanda yake gudun hijira, ya mutu.

Wani kakakin kungiyar da Muryar Amurka ta tuntuba, ya dage cewa shugaban kungiyar "yana nan daram da ransa", yana cewa rade -raden wai ya mutu ana yayata su ne domin a tilastawa shugaban ya fito daga mabuyarsa.

Ahalinda ake ciki kuma, gwamnatin Afghanistan tana binciken rahotannin cewa Mullah Omar ya mutu. Da yake magana da manema labarai nan a Kabul, kakakin shugaban kasar Syed Zafar Hashimi, ya ce "muna sane da rahotannin dangane da mutuwar Mullah Omar, shugaban kungiyar Taliban. Muna kan tantance rahotannin... ". Yace zai yi magana idan aka sami karin bayani kan tantancewar.

Wasu majiyoyi da masaniya kan shawarwarin sulhu na Afghanistan din, sun yi watsi da rahotanni mutuwar Mullah Omar, suna masu cewa ana hakan ne da nufin wargaza shawarwarin, a zama na biyu da ake shirin yi a Pakistan.

Amma kamar yadda gwamnatin kasar tayi alkawari dazu dazun nan ta fito fili ta tabbatar da mutuwar Mullah Omar

XS
SM
MD
LG