Kungiyar Taliban ta ce tana fatan a yau Lahadi za a kammala tattaunawar da take yi da Amurka, wacce za ta ba da damar a cimma matsaya kan yadda za a kawo karshen yakin Afghanistan da aka kwashe shekaru 18 ana yi.
Zaman tattaunawan tsakanin bangarorin biyu da ke takaddama, wanda ake yin shi a karo na tara, ya gudana ne a inda aka saba yin taron, wato kasar Qatar da ke yankin tekun Fasha.
Tawagar Amurka ta samu jagorancin jami’in diplomasiyya Zalmay Khalilzad, wanda ba’amurke ne dan asalin kasar ta Afghanistan.
A jiya Asabar, kakakin Taliban Zabihulla Mujahid, ya fadawa Muryar Amurka cewa, bangarorin biyu suna kokarin shata yadda dakarun da Amurka ke jagoranta za su janye daga kasar ta Afghanistan.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 25, 2023
Mawakiya Yar Najeriya Ta Yi Tarihi A Bikin Bada Lambar Yabo Na Oscar
-
Janairu 13, 2023
Lisa Marie Presley, Diyar Mawaki Elvis Ta Rasu
-
Janairu 11, 2023
Ana Tsaftace Yankunan Da Mahaukaciyar Guguwa Ta Ratsa A California