Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afirika Ita Tafi Kowacce Nahiya Karuwar Yawan Matasa A Duniya


Asusun Bill da Melinda Gates sun bada hujjar cewa Afirika tafi kowacce nahiya karuwar yawan matasa a duniya

Afirika ita tafi kowace nahiya karuwar yawan matasa a duniya, kuma kuma tana daya cikin kasashe 10 na duniya da ke da talauci, wanda a sanadiyar haka ya zama wajibi a saka ta cikin kasashen masu matukar neman taimako a duniya

Asusun Bill da Melinda Gates, sun bada wannan hujja ne a wani rahoton shekara shekara akan ci gaban da aka samu wajen cimma burin wannan karni mai dorewa wanda Majalisar dinkin duniya ta tsaida a wa’adin cimma wannan buri kan shekarar 2030.

Wannnan rahoton da aka gabatar Talata ya bukaci a auna Afirika da irin zuba jarin daya taimaka wajen dago kasashen China da India, wadanda a da suke cikin talauci kuma a yanzu suka shiga rukunin kasashe masu matsakaicin kudaden shiga.

Kashi sittin cikin dari na yan Afirika suna kasa da shekaru ashirin da hudu da haihuwa, yawan da Melinda Gates ta jaddada a wata hirar wayar talho da sashen turanci na Muryar Amurka ya yi da ita a farkon wannan wata.

Idan da duniya zata dauki matakin daya kamata wajen saka jari akan harkokin lafiya,da abinci mai gina jiki da ilimi a Afirika a cewar ta, da an samu yiyuwar wata zuri’a da zata bada mamaki a nan gaba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG