Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afirka ta Kudu Ta Janye Jakadanta Daga Israila


Falasdinawa dake zanga zanga
Falasdinawa dake zanga zanga

Saboda kisan gillar da sojojin Israila suka yiwa Falasdinawan dake zanga zangar kin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Kudus, kasar Afirka ta Kudu ta janye jakadanta daga kasar ta Israila

Afirka Ta Kudu ta janye Jakadanta daga kasar Isira’ila jiya Talata, bayan da sojojin Isira’ila su ka kashe 60 daga cikin Falasdinawan da ke zanga-zanga akan bude ofishin Jakadancin Amurka a birnin Kudus da ake takaddama a kai.

Sashin Harkokin Cudanyar Kasa da Kasa da Hadin Kai ya yi Allah wadai da matakin da sojojin Isira’ila suka dauka game da Falasdinawan da ke zanga-zanga a Gaza, da cewa, “Wadanda abin ya rutsa da su na zanga-zangar lumana ne kan takalar da Amurka ta yi, ta wajen kaddamar da Ofishin jakadancinta a Birnin Kudus.”

Wannan tashin hankalin, a cewar Sashin, ya sa Afirka ta Kudu ta gaggauta janye jakadanta daga Tel Aviv, inda akasarin Ofisoshin Jakadancin kasashe su ke a kasar Isira’ila.

Masu zanga-zangar, wadanda yawansu na saye da riguna masu dauke da sakon da ke cewa, “A ‘Yantar da Falasdinu” da kuma wanda ke cewa, “A Tsai Da Manufofin Wariya Na Isira’ila” --- ciki har da wata ‘yar kungiyar mutanen da ke kiran kansu Yahudawan Afirka Ta Kudu ‘Yan Rajin ‘Yantar da Falasdinawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG