Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afirka ta Kudu za ta samo wutar lantarki daga gawayin kwal


Afirka na bukatar karin makamashi don gudanar da harkokinta

Rahotanni daga Afirka ta kudu na cewa Gwamnatin kasar zata karfafa ginin injin samar da wutar lantarki mai aiki da kwal.

Rahotanni daga Afirka ta kudu na cewa Gwamnatin kasar zata karfafa ginin injin samar da wutar lantarki mai aiki da kwal.

Jiya Juma’a ce shugaba Jacob Zuma na Afirka ta kudu ya bayyana hakan a ziyarar gani da idon da ya kai inda ake shirin kafa injin na samar da wutar lantarkin.

Dubban ‘yan Afirka ta kudu ne suka yi dafifi cikin murna da farin cikin taren shugaba Jacob Zuma lokacin da ya isa Lephalale, yankin da Gwamnatin Afirka ta kudu ke son gina masana’antar samar da wutar lantarki mai aiki da Kwal.

Tazarar wurin da birnin Johannesburg kilomita 350 ne. Shugaban na Afirka ta kudu yaje ne bayan kammala bikin bude cibiyar farko da aka kammala aiki.

A jawabin da yayi shugaban Afirka ta kudu ya yiwa al’umma cikakken bayanin dalilin da yasa ake kokarin kafa wnanan masana’anta ta samar da wutar lantarki mai amfani da Kwal.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG