Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afrika Na Baya A Yaki Da Cutar Kanjamau


Michel Sidibe, Darektan yaki da cutar Kanjamau na Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban cibiyar yaki da cutar kanjamau ta Majalisar Dinkin Duniya yace gwajin kwayar cutar kanjamau yana da muhimmancin ga cimma gurin shawo kan cutar kafin shekara ta dubu biyu da talatin.

Sai dai jami’in Majalsar Dinkin Duniya ya shaidawa Muryar Amurka cewa, camfi da tsangwama da ake yiwa wadanda ke dauke da cutar kamjamau da kuma wadansu cututuka makamantan haka, na zama barazana ga cimma wannan burin a kasashe da dama.

Shekaru kalilan da suka shige, yana da wuya a ba dukan wadanda ke dauke da cutar maganin yakar kwayar cutar kanjamau ko kuma cututukan da suke fama dasu, amma yanzu, jami’ai suna kyautata zaton shawo kan cutar baki daya nan da shekara ta dubu biyu da talatin.

A shekara ta dubu biyu da daya, a Afrika ta Kudu, mutane casa’in ne kawai suke shan magani a cibiyoyin gwamnati, amma yanzu akwai kimanin mutane miliyan hudu da dari uku dake shan magani.

Michel Sidibe jami’in Majalisar Dinkin Duniya dake kula da yaki da cutar kanjamau a kasashen duniya, yace an sami ci gaba sabili da hadin kai da ake samu tsakanin kasashe da kuma tsakanin hukumomin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu. Idan aka kara samar da magunguna masu inganci da kuma samar da kafofin jinya, galibin kasashen nahiyar Afrika suna kan hanyar shawo kan wannan matsalar, sai dai ba dukansu bane

An bar Afrika ta yamma, da Afrika ta tsakiya, baya kwata-kwata. Yayinda muke da kashi sittin da daya cikin dari a fadin duniya baki daya dake samun magani, muna da kashi talatin da biyar ne kawai cikin dari da ake yiwa jinya a wadannan yankunan

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG