Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afrika Ta Zama Nahiya Mai Saurin Samun Ci Gaba-Inji MDD


'Yan Afrika

Nahiyar Afirka ta zamanto nahiyar da take saurin ci gaba a duniya. Cikin shekaru goma sha biyar masu zuwa, Majalisar Dinkin Duniya(MDD) ta yi hasashen birane goma masu saurin ci gaba suna Afirka.

A kasashen kudu da hamadan Afrika, yawan al’umma ya ninka tun tsakiyar shakarun alif da dari tara da casa'in. Yawan mutane sun kai miliyan dari hudu a shekarar 2016. A cewar masana, kashi 40 cikin 100 na mutanen yakin suna zaune a birane ne, inda aka kwatanta shi da kashi 31 cikin 100 a shekarar 2000.

Duk da haka, ci gaba ta fuskar gine-gine da kamfanoni bai kai yadda ake bukata ba domin ci gaba da gudanar da rayuwa a birane.

Kashi 60 cikin 100 na mutanen da ke zaune a birane a kasashen kudu da hamada suna zaune ne cikin yanayin na talauci, kashi 25 ne kadai ke samin taceccen ruwan sha.

Rashin kyan tsarin kwatoci da kuma rashin iya shawo kan ambaliyar ruwa suma wasu kalubale ne. Kouman Kossia Tamia sarauniyar gargajiya ce a Ivory Coast. Tana jin tsoron duk damunar da ta zo da kuma ambaliyar da ke faruwa.

Ta yi kukan cewa idan lokacin damuna yazo, ba zata iya yin komai ba. Komai ya tsaya cik.

Amadou Diarra shine magajin garin Arewacin Pikine, wata unguwar waje dake babban birnin Senegal, Dakar. Ya ce yana kallon yadda ake zuwa bandaki a kowa ina a waje, a matsayin matsalar dake ci gaba.

Ga fassarar rahotan Wakilin Muryar Amurka Nicolas Pinault:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG