Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sudan Sun Caccaki Wani Jami'in Amurka


‘Yan kasar Sudan sun caccaki wakilin Amurka a kasar saboda yin liyafa tare da daya a cikin mutane da ake musu kallon masu ruruta yaki a kasar.

Jakadar Amurka a Sudan Steven Koutsis ya halarci liyafar cin abincin bada baki na watan Ramadan a ranar Asabar tare da Mohamed Hamdan Dagolo, wanda ake zargin sojojinsa da aikata tu’annati a yankin Darfur da ma wasu wurare, cikin har da abubuwa da suka faru nan da ‘yan makwanni.

Dagolo da aka fi saninsa da lakabi Hemeti, shine komandan rundunar ‘yan bindiga ta Rapid Support Forces. A baya, Hemeti shine komandan ‘yan bindigan Janjaweed, wanda ake zargi da aikata kisar kare dangi a Darfur sama da shekaru goma da suka shude.

A waccan lokacin Amurka da sauran kasashen duniya sun yi Allah wadai da kisar a Darfur kana suka kira da gurfanar da wadanda suka aikata haka gaban doka.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG