Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ahmadinejad Ya Aikawa Da Trump Budaddiyar Wasika


Tsohon shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad
Tsohon shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad

Tsohon shugaban Iran mai tsatsauran ra'ayi Mahmud Ahmadinejad, ya wallafa wata budaddiyar wasika da ya aikawa da shugaban Amurka Donald Trump cikin harshen Ingilishi da Farsanci inda ya yaba mai kan fitowar da ya yi, ya bayyana "tsarin mulkin dimokradiyar Amurka a matsayin abinda ke cike da cin hanci."

Doguwar wasikar wacce aka wallafa a yau Lahadi, ta kuma soki shugaba Trump kan matakin haramtawa wasu kasashen bakwai shiga Amurka, ciki har da Iran, ya na mai cewa "Amurkan yau ta kowa da kowa ce."

Koda ya ke shugaba na Iran, ya yi la'akkari da yawan 'yan kasar ta Iran da yawansu ya kai miliyan daya da suka shiga kasar ta Amurka.

Ahmadinejad ya kuma soki yadda Amurka ta mamaye Majalisar Dinkin Duniya da yadda ya ce take katsalandan a harkokin kasashen duniya, lamarin da ya ce "ya haifar da rashin tsaro da yaki da rarrabuwar kawuna da kashe-kashe."

Ko a baya tsohon shugaban na Iran,ya taba rubutawa tsofaffin shugabannin Amurka wasika da suka hada da Barack Obama da George W. Bush.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG