Abubuwan tashin hankalin da wasu yara kimanin 800 su ka gani lokacin da aka yanka iyayensu a gabansu da sauran abubuwan rashin imani na Boko Haram, sun sa sun sami motsin hankali har su na ta wasu abubuwan da su ka sa aka lura cewa su na bukatar kwararru su binciki tunaninsu.
Don haka Hukumar Ilimin Firamare ta Bai Daya (ADSUBEB, a takaice), ta dau nauyin kulawa da wadannan yaran. Shugaban Hukumar ta ADSUBED Alhaji Dauda Fure ya bayyana cewa matsalar ta shafi yara sama da 2,000 wadanda su ka fito daga Kananan Hukumomi wajen 6. Ya ce matakan da su ka dauka na kulawa da yaran sun hada da tura su makaranta da sauran matakan kulawa.
Wakilinmu na jihar Adamawa wanda ya tura da labaran Ibrahim Abdul’aziz, y ace a daidai lokacin da ake samun wannan matsalar, wasu daidaikun ‘yan Nijeriya da kungiyoyi na cigaba da kai gudunmowa ga yaran. Na baya bayan nan shi ne taimakon magunguna na kudi Naira Miliyan 135 da matan gwamnonin jam’iyyar APC su ka kai.