Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Aikin Gyara Tashar Jiragen Sama Na Yamai


Taswirar Yadda Za A Mayar Da Tashar Jirgin Saman Yamai
Taswirar Yadda Za A Mayar Da Tashar Jirgin Saman Yamai

An yi bukin kaddamar da ayyukan kwaskwarima a filin jirgin saman Yamai wanda ke bukatar canjin fuska daga tsohon yayi zuwa irin na zamani ta yadda za a fita kunya a yayin taron shugabannin kasashen Afirka da ake saran gudanarwa a Nijar a shekarar 2019.

Ministan sufurin Nijar, Karidjo Mamadou yace gani suka yi ya kamata a yi gyaran tashar jirgin saman domin karban manyan baki kuma aikin zai samar wa matasa abin yi.

Miliyan 100,000 na CFA ake saran kashewa domin gudanar da wadannan ayyuka da aka damkawa kamfanin Soumma na kasar Turkiyya nauyin gudanarwa kuma a cewar wakilin kamfanin, za a kammala kafin shudewar wa’adin watanni sha biyun da aka alkawali inji shi.

Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou wanda ya aza tubulin farkon soma wadannan ayyuka ya ce ba shi da shakku a game da kwarewar kamfanin Soumma bisa la’akkari da ayyukan da ya yi a can baya a wasu kasashen Afirka irinsu Senegal, Equatorial Guinea da sauransu.

Jama’ar da suka halarci wannan biki sun yi na’am da wannan yunkuri na gwamnatin Nijar.

A cewar Adamou Imran Maiga, wannan babban alheri ce ga kasa. Sai dai ra’ayoyi sun sha bamban a tsakanin ‘yan Nijar game da tasirin wadannan ayyuka da wasu ke yi wa kallon wata hanyar kashe-mu-raba kasancewar tuni aka sayarwa wasu Turkawa hannun jarin wannan filin jirgi akan miliyan 100,000 na CFA. Alhaji Salisu Adamou jami’in fafutukar kare hakkin dan adam.

Shekaru a kalla 30 za a shafe wadannan Turkawa na tafiyar da harkokin filin jirgin saman na Diori Hamani a karkashin wannan tsari yayin da a dai bangare a yau Juma’a hadin guiwar gwamnatin Nijar da kamfanin Soumma ke kaddamar da ayyukan gina wata babbar otel a tsakiyar Birnin Yamai wacce ke zama masaukin shuwagabanin kasashen da zasu ziyarci nijer a albarkacin taron kungiyar AU na 2019.

Saurari rohoton

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG