Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aikin Haji: Hukumar Alhazan Najeriya Ta Ce Ta Kintsa


Aikin Hajji

Yayin da Alhazai ke harama, Hukumar Alhazan Najeriya ta ce ta kintsa tsab don tinkarar duk wata mtsala da ka taso. Ta ce burinta shi ne alhazan Najeriya, wadanda su ka kai kimanin dubu 80, su yi ayyukan ibada cikin natsuwa.

A yayin da ake gab da fara muhimman ayyukan ibada a hajjin bana, hukumar Alhazan Najeriya ta ce ta shirya tsab tun tinkarar duk wata matsala da ka taso saboda alhazan Najeriya wajen dubu 80 su samu gudanar da ayyukan ibada cikin natsuwa.

Alhazan Najeriya, kamar sauran alhazai daga sassan duniya su wajen miliyan biyu, sun kama hanyar zuwa Muna don fara muhimmin fanni na aikin na haji, na samun kulawa sosai a cewar Abdullahi Salame, Shugaban Kwamitin Wakilai da ya sa ido kan shirin aikin hajjin na bana. Ya ce an tanadar ma kowane alhaji abin sanyaya masa yanayi kuma an samar da motoci masu na’urar sanyaya wuri.

Baya ga sauran abubuwan kyautata aikin hajjin na bana, an kuma ba da bangaren lafiyar maniyyata muhimmnaci. Dr. Ibrahim Kana, mai kula da bangaren lafiyar mahajjata, ya ce baya ga tanada isassun magunguna, an kuma raba ma’aikatan jinya zuwa jahoji saboda a samar da cikakkiyar kulawa.

Ga Madina Dauda da cikakken labarin:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:59 0:00

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG