Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aikin Shimfida Layin Gas Na AKK Zai Bunkasa Tattalin Arzikin Najeriya - Masu Ruwa Da Tsaki


Farouk Ahmed
Farouk Ahmed

A yayin da ‘yan Najeriya ke fama da tsadar kayayyakin da suka shafi makamashi kamar iskar gas, man fetur da wutar lantarki, tare da hauhawar farashin da ake samu kusan kullum, gwamnatin kasar ta ce za’a sami walwala nan ba da jimawa ba.

Wannan na zuwa ne bayan tabbacin da kamfanin da ke shimfida layin iskar gas na Ajaokuta, Kaduna zuwa Kano wato AKK tare da hadin gwiwar kamfanin NNPCL suka bayar, na cewa za’a karasa aikin a watan Yuli ko Agustan shekarar 2024 mai zuwa.

Matsalar tsadar makamashi a Najeriya abu ne da ke ci gaba da ciwa al’ummar kasar tuwo a kwaryar musamman ma tashin farashin iskar gas da man fetur da ake gani a baya-bayan nan.

An sami karin kaso 19.3 na gangar mai a kasuwar duniya a karshen watan Satumba wanda ya sa kudin sauke man zuwa Naira 596.93 a kan kowace lita, daga kusan Naira 500 a watan Yulin shekarar 2023, Hakan ne ya haddasa karin farashin kowacce lita a gidajen sayar da mai a kasar.

Farouk Ahmed da Tawagar rangadin AKK
Farouk Ahmed da Tawagar rangadin AKK

A yayin rangadin duba aikin shimfida layin iskar gas na AKK a yankin Kwali na birnin tarayya Abuja, mataimakin shugaban kamfanin NNPCL a fannin iskar gas, Olalekan Ogunleye, ya ce bututun iskar gas na Ajaokuta da zai ratsa ta wani bangare na Abuja, Kaduna da Kano, aiki ne na bunkasar tattalin arziki.

Ya kuma ce NNPCL na ba da fifiko kan tabbatar da karasa aikin a kan lokaci, tare da hadin gwiwar kamfanin da aka baiwa kwangila wato Oilserv da sauran masu ruwa da tsaki da cikakken goyon baya daga gwamnatin tarayya.

Ya kara da cewa yana taya ’yan Najeriya murna tare da jinjina ga gwamnatin kasar kan goyon bayan da aka baiwa NNPCL, kuma bunkasar tattalin arziki Najeriya na nan tafe.

Farouk Ahmed da karamin Minista EEkpe
Farouk Ahmed da karamin Minista EEkpe

A nasa bangare, karamin ministan albarkatun man fetur a fannin iskar gas, Ekperikpe Expo, ya jaddada mahimmancin shimfida layin iskar gas na AKK yana mai cewa a yau, duniya ta amince da iskar gas a matsayin gagarumin sauyi a fannin makamashin kuma ko shakka babu shugaban Najeriya ya bayyana karara cewa iskar gas ne sabon man fetir.

Kazalika, Ekpo yace iskar gas na wakilcin makamashi kuma dole ne a ba da mahimmanci wajen aikin shimfida layin gas na AKK don tabbatar da cewa dukkan jihohin kasar sun sami iskar gas.

Shugaban hukumar NMDPRA mai kula da dokokin fannin albarkatun man fetur da iskar gas ta Najeriya wato NMDPRA, Injiniya Faruk Ahmed, ya ce aikin babban alheri ne ga jama’ar Arewa da ma kasar baki daya, ganin yadda aikin zai farfado da masana’antu, samar da ayyukan yi ga matasa da dai sauransu.

Wasu mazauna yankin da ake gudanar da aikin sun bukaci gwamnati ta karasa aikin a kan lokaci doń ‘yan kasa su fara cin moriyarsa.

Masana dai sun ce, idan aka karasa aikin, bututun na iya jigilar iskar gas cubic biliyan biyu a kowace rana zuwa kamfanonin samar da wutar lantarki masu zaman kansu guda uku da za’a samar a Abuja, Kaduna, Kano, da sauran masana'antu masu amfani da iskar gas da kuma wasu da aka gano tare da neman ‘yan kasuwa da zasu shiga cikin tsarin.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG