Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aisha Buhari Ta Caccaki Jami'an Tsaron Najeriya


Sojojin Najeriya a jikin baburan da zasu rika shiga daji da su wajen yakar 'yan Boko Haram

Uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta yi kira ga hukumomin jami’an tsaron kasar da su yi gaggawar magance matsalar tsaron ‘yan bindiga da ta addabi wasu sassan Najeriya.

Rahotanni da dama sun ruwaito cewa, Aisha ta yi kiran ne, a yau Asabar yayin da ta kai ziyara jihar Katsina domin raba kayan tallafi ga wadannan hare-haren ‘yan bindiga ya shafa.

Yankin karamar hukumar Batsari, na daga cikin yankunan da suka yi fama da hare-haren 'yan bindiga a 'yan kwanakin nan, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Aisha ta ce, lokaci ya yi da ko a kawo karshen ‘yan bindigar, in ba haka, su ‘yan bindigar za su kawo karshen mutane, kamar yadda shafin yanar gizo na Sahara Repoters ya ruwaito.

Uwargidan shugaban kasar, ta kuma kalubalanci duk masu karfin fada a ji, da su fito su fadi abubuwa da suke faruwa marasa dadi a Najeriya, domin mahukunta su dauki mataki akai.

Jaridar Punch ta ruwaito uwargidan shugaban kasar tana cewa, "ya zama dole mu yi magana kan duk abin da ke faruwa wanda bai dace ba."

Ba dai yau Aisha ta fara sukar lamirin gwamnatin mijinta ba, ko a ‘yan kwanakin nan wasu rahotanni sun ruwaito ta tana sukan matakin kashe dala miliyan 16 wajen sayen gidan ragar sauro.

A kuma shekarun baya, ta taba fitowa ta soki gwamnatin mijinta, inda ta yi korafin cewa wasu mutane kalilan sun karbe ragamar tafiyar da gwamnati, kalaman da shi kansa Buharin ya musanta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG