Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aisha Buhari Ta Kalubalanci Matan Arewa Kan Neman Ilimin Boko


AISHA BUHARI

Uwargidan shugaban Najeriya, Hajiya Aisha Buhari, ta bukaci matan arewacin kasar da su tashi haikan don neman ilimin Boko domn samun damar cin moriyar abubuwan da gwamnati ke shiryawa don inganta rayuwar ‘yan kasa musamman mata da matasa.

Hajiya Aisha Buhari ta yi wannan kira ne a jihar Bauchi wajen bikin yaye rukunin mata da matasa har dubu ‘daya, da aka koyawa sana’o’i iri daban-daban domin su sami abin dogaro da kai.

A nata jawabin mai dakin gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Hadiza Mohammad Abudullahi Abubakar, tace jihar Bauchi na alfahari da irin gudunmawar da suke samu daga shirin tallafin da Aisha Buhari ke baiwa jihohin kasar.

Gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar, yayiwa Hajiya Aisha godiya saboda kirkiro gagarumin shirin baiwa mata hanyoyin koyon sana’a don gogaro da kai.

Wakiliyar mata da matasa da suka amfana daga wannan shiri, Rabi Usman, tace a madadin duk mata da matasan da suka koyi sana’o’i karkashin shirin suna mika sakon godiyarsu.

Sai dai kuma shugaban kungiyar kare muradun nakasassu a Najeriya, Hamza Waziri Mohammad, yace su ma suna bukatar tallafin da zai sa su zamo masu dogaro da kai, a maimakon basu kekunan guragu dake sasu yawon bara.

Domin karin bayani ga rahotan Abdulwahab Mohammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG