Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hijabi: Sultan Ya Soki Matakin Hana Daliba Takardar Shaidar Zama Lauya


Wani taron mata a jihar Bauchi a lokacin bikin ranar Hijab ta Duniya
Wani taron mata a jihar Bauchi a lokacin bikin ranar Hijab ta Duniya

Ana ci gaba da sukar matakin da wata jami'a ta dauka na hana wata daliba shiga zauren rantsar da daliban lauyoyi da za su kama aiki, saboda ta saka hijabi hade da kayan lauya a jami'ar Ilori da ke jihar Kwara.

Sarkin Musulmi, Mai Martaba Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi tir da takaddamar da ta kunno kai kan hana wata daliba da ta saka hijabi shiga zauren rantsar da daliban lauyoyi inda aka ba su takardar shaidar kama aiki.

A makon da ya gabata ne aka hana Amasa Firdaus shiga wajen bikin a jam’iar Ilori da ke jihar Kwara, saboda ta sanya hijabi hade da kanayn aikin lauya.

Amma Sultan Abubakar ya ce, hijabi sutura ce da ke nuna kamala wanda addinin Musulunci ya umurci ‘ya’ya mata su saka, kamar yadda jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito.

A yau Asabar Sarki Abubakar, ya bayyana hakan a wani taron jama’ar Musulmi da aka yi a Legas a karo na biyar.

Sultan wanda shi ne shugaban Majalisar Koli ta Musulman Najeriya, ya kuma nuna takaici da fargabarsa kan yadda wannan lamari zai rika barazana ga ‘ya’ya mata masu saka hijabai, kamar yadda jaridar ta wallafa.

Masu ruwa da tsaki a wajen taron rantsar da daliban, sun hana Firdaus shiga zauren ne saboda a cewarsu shigar da ta yi da hijabi ya saba ka'ida.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG