Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aisha Buhari Ta Sha Suka Bayan Ta Wallafa Hotunan Zahra Buhari Na Kamalla Digiri A Intanet Alhalin ASUU Na Yajin Aiki

An Ta Yi Wa Aisha Buhari Suka Bayan Ta Wallafa Hotunan Zahara Buhari Na Kamalla Digiri A Intanet Alhalin ASUU Na Yajin Aiki
An Ta Yi Wa Aisha Buhari Suka Bayan Ta Wallafa Hotunan Zahara Buhari Na Kamalla Digiri A Intanet Alhalin ASUU Na Yajin Aiki

An yi ta sukar uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha a shafukan sada zumunta saboda ta yada hotunan, Zahra Buhari ta kammala karatun jami'a a yanar gizo.

WASHINGTON, D.C. - A gabatarwar, Aisha ta bayyana cewa Zahra ta kammala karatun digiri mai daraja ta farko ne a fannin ilimin gine-gine.

“Ina taya Misis Zahra B Buhari murnar kammala karatunki da lambar yabo ta ‘First Class’ a fannin Kimiyyar Gine-gine. Ina muku fatan Alkhairi,” a cewar Uwargidan shugaban kasar a shafinta na yanar gizo yayin da take yada hotunan bikin yaye daliban a shafukan sada zumunta.

An Kai Wa Aisha Buhari Suka Bayan Ta Wallafa Hotuna Zahara Buhari Na Kamalla Digiri A Intanet A Yayin Yajin Aikin ASUU
An Kai Wa Aisha Buhari Suka Bayan Ta Wallafa Hotuna Zahara Buhari Na Kamalla Digiri A Intanet A Yayin Yajin Aikin ASUU

Zahra ita ce matar dan Buhari, Yusuf Muhammadu Buhari. Idan za a iya tunawa Yusuf ya auri Zahra ne daga jihar Kano a watan Agusta 2021. Ita ce ta biyu cikin 'ya'yan Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero.

Wallafa wannan bikin kammala karatu da uwargidan shugaban kasar ta yi ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta yayin da masu amfani da yanar gizo suka bayyana ta a matsayin ba ta kyauta ba da yin irin wannan a daidai lokacin da aka hana dubban daliban Najeriya zuwa makaranta.

Idan an tuna, jami'o'in gwamnatin Najeriya sun kasance a rufe tun watan Fabrairun 2022 yayin da gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ke takun saka.

An Kai Wa Aisha Buhari Suka Bayan Ta Wallafa Hotuna Zahara Buhari Na Kamalla Digiri A Intanet A Yayin Yajin Aikin ASUU
An Kai Wa Aisha Buhari Suka Bayan Ta Wallafa Hotuna Zahara Buhari Na Kamalla Digiri A Intanet A Yayin Yajin Aikin ASUU

Kalaman wasu ga Aisha akan shafinta na Facebook:

Dimbo Atiya: “This is insensitive because there are millions of other children at home because of your husband’s incompetence. Let’s call a spade a spade.”

“Wannan rashin hankali ne saboda akwai miliyoyin yara a gida saboda kasawar mijinki. "

Fadima Ibrahim: “Am thoroughly disappointed in you posting this, after knowing full well our students have been at home for months due to your husband’s in competence and nonchalance.”

"Na ji takaici matuka da kika wallafa wannan, bayan kin sani sarai dalibanmu sun shafe watanni suna gida saboda kasawar mijinki da rashin sanin ya kamata."

Benjoe Katangwat: “How do you people feel seeing other children stucked at home with schools closed but still come publicly to show us how your children are graduating elsewhere? Anyway, congratulations to her.”

“Yaya kuke ji kuna ganin wasu yara sun makale a gida tare da rufe makarantu amma har kuna fitowa fili don nuna mana yadda yaranku ke kammala karatunsu a waje? Duk da haka, ina taya ta murna.”

Aisha Buhari Ta Sha Suka Bayan Ta Wallafa Hotuna Zahra Buhari Na Kamalla Digiri A Intanet A Yayin Yajin Aikin ASUU
Aisha Buhari Ta Sha Suka Bayan Ta Wallafa Hotuna Zahra Buhari Na Kamalla Digiri A Intanet A Yayin Yajin Aikin ASUU

XS
SM
MD
LG