Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutane 13 Suka Rasa Rayukansu


A wani mummunan hadarin mota a jihar Taraba akalla mutane goma sha uku suka rasa rayukansu yawancinsu konewa suka yi sabili da man fetur.

Akalla an tababatar da mutuwar mutane goma sha uku a wani hadarin mota da ya auku a kan hanyar Wukari jihar Taraba.

Bayanai sun nuna cewa hadarin ya auku ne yayin da wata mota da ta taso daga Gidin Dorawa suka yi taho mu gama da wata motar safa kirar makafolo. Yawancin fasinjojin dake cikin motar mata ne wadanda suka fito daga cin kasuwa. An ce motar na dauke da jarkoki na man fetur da kanazir. A kokarin kaucewa motar safar direban ya saki hannu sai ya afka daji inda ta buga itace nan take ta kama da wuta. Yawancin matan dake cikin motar suka kone. Nan take mata 13 sun mutu.

Wadanda suka samu suka tsira da rayukansu an garzaya da su babban aibitin garin Wukari yayin da kuma jami'an hukumar Road Safety ke hada alkaluman wadada hadarin ya rutsa da su. Mr. Peter Kigbo jami'in hukumar ya ce ya samu labarin hadarin amma yana jiran cikakken bayani.

Hadarin motoci a kan hanyoyin Najeriya ba wani abu sabo ba ne. Rashin hanyoyi masu kyau da tukin ganganci su ne umalubaisan yawan hadarin motoci.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:50 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG