Accessibility links

Shehun Borno Ya Yi Tur da Hare-haren da 'Yanbindiga Ke Kaiwa Kauyuka a Jihar Borno


Maimartaba Shehun Borno

Maimartaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Garbai Umar El-Kanemi ya yi alawadai da hare-haren da 'yanbindiga sukan kai kan kauyukan Borno da ma kauyukan jihar Adamawa

Cikin makwanni biyu ke nan da wasu 'yanbindiga da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka farma wasu kauyukan Borno da na Adamawa inda suka hallaka mutane da dukiyoyi da dama.

Kauyukan da aka kai hari sun hada da Alauo da Kawuri da kauyukan Adamawa dake makwaftaka da jihar Borno. Jihohin biyu na cikin jihohi uku da aka kakabawa dokar ta baci domin a dakile irin wadannan tashin tashinan amma har yanzu abun ya cutura.

A wannan makon ne shehun Borno Alhaji El-Kanemi ya ziyarci kauyukan da aka kaiwa hare-hare. Ya jajanta masu game da lamarin kuma ya nuna takaicinsa da abun da ya gani. Ya ce sai dai a cigaba da addu'a domin wadanda suka mutu ba zasu dawo ba. Ya ce tun da gwamnati ta kai sojoji da matasa 'yan sakai to ya kamata wadanda suka gudu su yi hakuri su koma gidajensu.

Shehu El-Kanemi ya kira masu hannu da shuni su dinga tallafawa wadanda irin wannan bala'in ya samesu. Kawo yanzu dai dubban mutane suka fice daga kauyukan da lamarin ya shafa suna fakewa da 'yanuwansu da abokanai da wasu kuma a sansanin 'yan gudun hijira da gwamnati ta tanada. Ya ce masu hali kada su zubawa gwamnati ido. Su ma su taimaka. Ya ce da yawan mutanen Kawuri ya fi dubu goma amma yanzu da kyar wadanda suka rage su kai dubu daya. Ya ce garin gaba daya an koneshi. Mutanen gari manoma ne. Abun da suka noma shi zasu ci su kai kasuwa su sayar domin rayuwar yau da kullun amma duk kayan nomansu an kone. Babu abun da ya rage.

Maimartaba ya ce koina a duniya ana samun rigingimu domin haka akwai bukatar komawa ga Ubangiji

XS
SM
MD
LG