Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutane 140 Yawancinsu Sojoji Sun Halaka A Afghanistan


An kai wani harin kunar bakin wake mafi muni a arewacin kasar Afghanistan

An bada rahoton cewa sumamen kunar bakin wake da kungiyar Taliban ta kai akan wani babban sansanin soja a arewacin kasar Afghanistan cikin dare ya kashe akalla mutane dari da arba’in, yawancinsu sojoji a hari mafi muni da aka kaiwa sojojin Afghanistan tun shekara ta dubu biyu da daya.

Shedun gani da ido sunce mutane goma cikin damarar harin kunar bakin wake sosai cikin motocin soja guda biyu, wadanda suka yi shigar burtu kamar sojojin gwamnati ne suka kutsa hedikwatar rundunar soja ta 209 jiya Jumaa a Mazar-i-Sharif hedikwatar lardin Balkh dake arewacin kasar.

Gidajen Talibijin sun ambaci kafofin soja da ba’a baiyana sunayensu dana yan siyasa suna fadi a yau Asabar cewa akalla sojoji arba’in ne aka kashe a harin da aka kai jiya juma’a da rana, akalla sojoji dari ne kuma suka ji rauni.

Jami’an yankin sun baiyana cewa maharan na kungiyar Taliban sun yi wa sojoji wanka da harsashe a lokacinda suke fitowa daga Masalaci bayan sunyi sallar Azar, a yayinda wasu maharan suka kutsa dakin cin abinci kafin sojojin kundubala suka yi musu kawanya, suka yi musayar mumunar harbe harbe.

Nan da nan mai magana da yawun kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid yayi ikirarin cewa kungiyar sa ce keda alhakin kai harin. A yau Asabar ya baiwa yan jarida karin bayani harma da hotunan wadanda suka kai harin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG