Accessibility links

Akalla mutane dubu talatin sun rasa matsuguninsu a arewacin Mali

  • Jummai Ali

Kwamitin kungiyar agaji ta kasa da kasa Red Cross yace, akalla mutane dubu talatin ne suka rasa mtsuguninsu a arewacin kaasar Mali, inda mayakan Buzaye suka kaddamar da sabuwar bore akan gwamnatin kasar.

Kwamitin kungiyar agaji ta kasa da kasa Red Cross, yace akalla mutane dubu talatin sun rasa matsuguninsu a arewacin kasar Mali, inda mayakan Buzaye suka kaddamar da sabon hari akan gwamnati kasar.

A ranar Laraba yan tawaye, Buzaye suka tilastawa sojojin gwamnati janyewa daga garin Tin Zaouatene dake kan iyakar kasar da kasar Algeria.

Tun lokacinda Buzayen suka kaddamar da hare hare a ranar sha bakwai ga watan Janairu sun gwabza da sojojin gwammnati a biranen arewacin kasar da dama.

Jiya wata tawagar wakilan kungiyar habaka tattalin arzikin Afrika ta yamma da ake cewa ECOWAS ta kai ziyara Bamako baban birnin Algeria domin nazarin yadda al'amurran jin kai suka kasance a arewacin kasar.

Drektan sadarwar kungiyar ECOWAS, Sonny Ugoh ya fadawa Muryar Amirka cewa, kungiyarsa tana fatar gwamnatin Mali ata yi shawarwari da Buzayen domin a magance wannan matsala.

Su dai yan tawayen Buzayen sunce suna neman yancin ci gashin kai daga gwamnatin kasar wadda cibiyarta ke kudancin kasar, da suka ce tayi watsi da yankin arewacin kasar mai hamada.

A kwanan nan daruruwan Buzaye suka koma arewaci Mali daga kasar Libya, inda suka fafata kafada da kafada da sojojin da suke biyaya ga tsohon shugaban Libya marigayi Moammar Gaddafi.

XS
SM
MD
LG